Bani da Hurumin Sasantawa Tsakanin Ganduje da Sanusi Lamido- Inji Buhari.

Bani da Hurumin Sasantawa Tsakanin Ganduje da Sanusi Lamido- Inji Buhari.

Daga Mohammed Lawal :

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai iya sasanta rashin jituwar dake tsakanin gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ba, domin kuwa kundin tsarin mulki bai bashi ikon yin hakan ba.

Jiya juma’a ne Shugaba Buhari yayi wannan furucin sa’ilin da yake karbar sabbin ‘yan majalisun  dokokin jihar su bakwai da aka zaba kwanan nan a karkashin jagorancin gwamna Ganduji a fadar shugaban kasar dake Aso Rock.

Shugaban na Nijeriya dai yana maida martini ne kan kiraye kirayen da wasu ‘yan Nijeriya keyi na yayiwa Allah da Annabi ya shiga tsakanin wadannan mutane biyu da suke takun saka da juna.

Ko ranar Alhamis din da ta gabata saida mai martaba sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya ya gabatar da rokonsa ga shugaban na Nijeriya da ya sa bakin domin ceto sarautun gargajiya na arewacin Nijeriya daga durkushewa ta hanyar magance rudanin da masarautar Kano ta shiga.

Da yake tsakoci a karo na farko a bainar jama’a kan wannan takaddama tsakanin mutanen biyu, shugaban Buhari cewa yayi kundin tsarin mulkin kasa bai bashi damar sanya baki ba a cikin wannan takaddama.

Yace “nasan rawar da zan iya takawa a matsayina na shugaban kasa”. A hukunce gwamnan jihar Kano yana da rawar da zai taka, matukar magana tana a gaban majalisar dokokin jiha, to shugaban kasa baya da hurumin yin shishshigi cikin lamarin, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0