Babbar hanyar warware rikici itace a zauna a tattauna – Inji Onaiyekan

Babbar hanyar warware rikici itace a zauna a tattauna – Inji Onaiyekan

Daga Kabiru Yusuf

Tsohon shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN, Cardinal John Onaiyekan ya ce ba wata hanya ta warware rikici da tabbatar da zaman lafiya sai hanyra zama a tattauna, inda ya ce ba abinda ya dace ga ‘yan Najeriya illa a kowane lokaci aka samu sabani, to abi hanyar sulhu domin samun zaman lafiya.

Cardinal Onaiyekan ya furta haka ne a jawabinsa a wajen bikin yaye daliban Cibiyarsa mai ikrarin samar da zaman lafiya na shekarar 2018/2019 wato Cardinal Onaiyekan Foundation for Peace (COFP) cibiyar da ta horar da dalibai akan shirya zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban,.

A cewar babban Limamin Kiristan, mutane zaka ji suna tambaya cewar A’a, wai me ke faruwa ne Cibiyar babban Limamin Kirista na ba wa sakataren kungiyar Miyetti Allah takardar shaida? Hakika haka abin yake, domin a tunaninsu babu zaman lafiya domin ba sa zatan za’a iya warware duk wani rikici da ya taso.

Amma sun kasa gane cewa duk wani rikici da ya taso, za’a iya warwae shi ne in har jama’a zasu amince a yi zama na fahimtar juna, a tattauna, kowa ya fahimci kowa ba tare da tunanin kabila ko addini ba. Don haka ni ina godiya ga Madaukakin sarki da ya sa wannan cibiya ta mu abinda ta sa a gaba ke nan.

Cibiyar dai ta yaye dalibai 35 a wannan karo, wadanda suka hada da Kiristoci 18, da kuma Musulmi 17, wadanda aka zabo su daga yankunan Najeriya 6. Haka kuma sun kushi maza 22 da mata 13 wadanda aka zabo su daga cikin kabilu daban-daban na kasar nan.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0