Ba za a samu zaman lafiya a Najeriya ba har sai…inji Farfesa Ango Abdullahi.

Ba za a samu zaman lafiya a Najeriya ba har sai…inji Farfesa Ango Abdullahi.

Daga Kabiru Yusuf.

Tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, Farfesa Ango Abdullahi wanda shine shugaban Kungiyar Dattawan Arewa ta ‘Northern Elders Forum’ a hirarsa da Moses Alao na Jaridar Tribune kan kace-na-cen da ake yi dangane da samar da wajen kiwo domin fulani Makiyaya wato RUGA, ya bayyana ra’ayinsa akan wannan batu da kuma wa’adin da hadaddiyar kungiyar samarin Arewar ta ba wa gwamnati na wata guda, da ta ci gaba da aiwatar da shirinta na Rugar da ta bada sanarwar dakatar da shi, da kuma matsalolin tsaro a kasa baki daya.

Ga kadan daga cikin abinda hirar ta.sa ta kunsa

Tambaya: Sakamakon dakatar da shirin gwamnati na RUGA, hadaddiyar kungiyar samarin Arewa ta nemii gwamnatin da ta ci gaba da shirinta nan da wata guda, dalilin da ya jawo wasu kungiyoyin irin su Ohanaze ta Inyamurai da Afenifere ta Yarabawa suma suka yi tasu barazanar, ko me zaka ce a kan haka?

Amsa : A takaice, matsayina shine, wannan batu na Fulani Makiyaya lamari ne da ke tare da mu tun shekaru 200 ko ma in ce 300. To, amma in wasu ‘yan Najeriya zasu mayar da shi na Siyasa, to su suka jiyo.


Tambaya: Kana nufin duk maganganun da ake kan rikici tsakanin Makiyaya da Manoma duk Siyasa ne? 


Amsa : Kwarai! ba wani Abu sai siyasa. Gwamnati ta kasa daukar mataki, mutane na mayar da lamarin siyasa. To, in haka za a ci gaba da yi kan shirye-shiryen gwamnati, shi ke nan.

Tambaya: Amma in ana maganar rikici tsakanin Makiyaya da Manoma kuma har ana maganar rasa rayuka, shin kana gani za’a kira shi da siyasa?


Amsa : Ka ga ni na fada maka cewar Makiyaya da Manoma suna tare tun fiye da shekaru 300 kafin zuwan Turawa. Me yasa sai yanzu ne ake samun hakan? Wannan lamari ne da kowa ya sani. Amma ana so a mayar da shi siyasa, shi ke nan.

Tambaya: Amma kungiyarku ta Dattawan Arewa itama ta ja kunne kan haka..

Amsa : Kungiyar mu ta zauna ta rubata rahoto akan wannan matsala tun lokacin da gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom yake kokarin kafa doka akan lamarin wacce shi da kansa ya san  ba abu ne me yiwuwa ba. Mun neme shi da ya dan dakata tukunna, ko ma samu mu ba shi shawara kan matsalar a matsayinmu na masana kan lamarin, amma ka mun mu mika rahotanmu ya riga ya aiwatar da dokar, lamarin da ya jefa jihar cikin rashin halin rashin hankali. Ka ga duk wannan ba shi da amfani. A haddasa rikici a kasa da kuma cikin jihohin. Abin takaici ne, ni banga yadda matsala kankanuwa za’a yi ta jujjuyata ba har sai ta koma babban.

Tambaya: Ka ce kankanuwar matsala. A nan kana nufin samar da wajen kiwan na RUGA ba wani abu ba ne, in ka dubi abinda shugaban kungiyar Yarabawa ta Afenifere ya fadi kan fulani , wadanda suka kwace garin  Ilorin daga hannun Afonja. Me zaka ce kan wannan? 


Amsa : Eee, hakane kuma gaskiya ne Fulani sun ci garin Ilori lokacin jihadi. Amma Karka manta da cewar Akwai Fulani a Ilori tun da can domin mafi yawancin Mutanan Ilori ai Fulani ne tun farko. Kai daI kawai sai dai a ce suna.magana ne da yaran Yarabanci, amma Fulani ne. Gaskiya ne, mun dade da sanin tarihin Afonja da Fulani a garin Ilori.

Tambaya: Amma tsoran shine, in an bari Fulani zasu kwace garuruwan mazauna kudancin Najeriya ke nan, in aka basu filin kiwo…

Amsa : (Uhum) Karka manta harkar kiwo da noma sune abinda na yi fice. Ka tuna na zama daraktan cibiyar aikin Gona ta jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria. Na yi shekaru da dama kafin na zama shugaban jami’ar Ahmadu Bello. Domin haka duk wani bayani na sirri kan aikin Gona da kiwo, wani kace na ce ba zai bada abinda ake so ba. Baya haka ma kashi 35 ne kacal na kasar nan ake iya nomawa, kashi 65 ba a amfani da shi. Saboda haka dole ne sai an tashi tsaye wajen bunkasar noma da kiwo ne mutane kasar nan zasu rabu da talauci. In kuma ba haka ba, to lallai zaman lafiya baza mu same shi ba.


Tambaya: Ganin cewa yanzu gwamnati ta dakatar da wannan shirin na RUGA, kuma sai gashi wasu kungiyoyin daga Arewa ciki kuwa har da kungiyar Miyatti Allah na barazanar lallai sai gwamnati ta dawo da wannan shiri, ko me kake gani? 

Amsa : A har kullum ni a wajena wannan gwamnati ta gaza. Domin gwamnati a kullum gazawa take a al’amuranta ciki kuwa har da shi wannan shirin na RUGA.

TAMBAYA: wato kana Zargin Buhari da gazawa ke nan, saboda ya dakatar da shirin da ya kawo kace-na-ce a kasa ke nan? 

Amsa : Ba haka nake nufin ba. Ina nufin gwamnati bata tsaya ta yi kyakkyawan shirin ba tun da farko. Na bayyana haka a gaban mataimakin shugaban kasa da Ministan aikin Gona. Domin ya kamata a ce sun kira taron majalisar hukumar aikin Gona da kwamishinonin aikin Gona na jihohi. Su zo su zauna su tsara shirin, domin Fulani Makiyaya ba a waje daya ko jiha daya suke ba. A ko’ina suke a kasar nan. Saboda haka wannan matsala ce ta kasa baki daya kuma wajibi ne a samu mafita ta kasa baki daya, ba wai wata jiha daya ta tsara dokar ta ba. Wanda yin hakan baya kan ka’dojin dokar kasar.

Akwai maganganu da dama da ake yi na cewa, Najeriya kasa daya ce, Al’uma daya. Kuma kowane Dan Najeriya yana da ikon zama a ko’ina cikin Najeriya kuma yi sana’arsa ba tare da tsangwama ba kamar yadda tsarin mulki ya tanada. Amma abun ba haka yake ba in an lura da yadda a wasu jihohi ake tsangwamar Fulani, an hana su neman abinci. Haka bai dace ba, kuma baza a yadda da haka ba.

Za mu sa aya a nan, Sai nan gaba za mu ci gaba.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0