Arewa Maso Gabas Zata yi Koyi da Daga Japan Wajen Sake Gina Yankin.

Arewa Maso Gabas Zata yi Koyi da Daga Japan Wajen Sake Gina Yankin.

Balarabe Abubakar

Sama da shekaru 10 da aka shafe ana yakin boko haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya yasa ake bukatar wasu dabaru da kwarewa kafin asake gina yankin da kuma farfado da tattalin arzikin ta.

Hakan yasa hukumar kula da aiyukan cigaban kasa ta Japan Jica,ta shirya taro a Abuja don musayar darasi kan dabarun da ta bi wajen sake gina Hiroshima bayan yakin duniya na biyu wanda tabbas zai taimaka wa yankin.

A yadda ake kokarin farfadowa da sake gina yankin arewa maso gabashin Najeriya wanda harma hukuma ta musamman gwamnatin kasar ta samar don haka, yasa yake da matukar mahimmanci ta samu darussa daga kasar Japan kan dabarun da tabi wajen sake ginin Hiroshima bayan yakin duniya na biyu.

Mataimakiyar wakilin kasa na sashen inganta cigaban kasa na majalisar dinkin duniya UNDP Carine Yengayenge ta shaida cewan wannan zaiyi matukar tasiri ga sake gina yankin arewa maso gabas.

Shugabar tawagar hukumar kula da aiyukan cigaban kasa ta Japan Jica   Matiko Kora tayi bayanin cewa da hadin guiwar majalisar dinkin duniya mun shirya abubuwan da dama ga yankin arewa maso gabashin Najeriya, wanda zasu amfanar da dumbin darasin da suka samu wajen gina Hiroshima bayan yakin duniya na biyu.

Daga cikin tawagar gwamnati daga yankin arewa maso gabas Jaridar Hantsi ta zanta da shugaban sabuwar hukumar sake gina jiha na jihar Yobe Dr.Goje Mohammed inda yace daya daga cin babban abun da suka koya shine, Japan ta tattara kayan tarihi don nunawa masu tasowa gaba, don susan ga abun da ya faru kuma ga hanyoyin da aka bi wajen sake ginawa da kuma farfado da gurin.Hakazalika  suka dauki jagorancin sake gyara gurin da kansu.

Abu na uku kuma shine kishin kasa,sun nuna cewan lallai idan babu kishin kasa bazai yiwu ba.

Ana dai fatar Najeriya tasa kishin kasa cikin wannan aiki kamar yadda Japan tayi ,inba haka ba tasirin kalilan ne.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0