Arewa Bata dace da Shugabanni na Gari ba.–Sanusi

Arewa Bata dace da Shugabanni na Gari ba.–Sanusi

Daga Mohammed :

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi ya bayyana takaicinsa bisa ga yadda matsanancin talauci da jahilci ya yiwa arewacin Nijeriya dabaibayi, ta yadda babu wani shugaba a yankin na arewacin Nijeriya da zai bugi kirjin cewa ya gamsu da shugabancin sa.

Jiya litinin ne Sanusi yayi wannan furuci a garin Kaduna, a wajen bukin tunawa da ranar haihuwar gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.

Yayi kira ga shugabannin na arewacin Nijeria da su zuba makudan kudade a fannin ilimi tare da maida hankali wajen rage radadin talauici tsakanin al’umma. Yace babu wani shugaba a arewacin Nijeriya da zai bugi kirji yace yana farin ciki bisa ga halin da arewacin kasar ke ciki, musamman yadda kashi 87 na al’ummar ke cikin talauci.

 Ya kara da cewa babu yadda za’ayi kayi farin ciki yayin da miliyoyin kananan yara a arewacin kasar basu zuwa makaranta, suna yawon bara, gami da matsalar shan miyagun kwayoyi tsakanin matasa, da ‘yan bangar siyasa da kuma uwa uba matsalar Boko Haram.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0