APC ta ga samu ta ga rashi a Zamfara

APC ta ga samu ta ga rashi a Zamfara

Mohammed Lawal

Yayin da kotun koli ta tarayyar Nijeriya ta zartar da hukuncin soke nasarar da jam’iyyar APC ta samu a jihar Zamfara bisa ga wasu kwararan dalilai da ta gabatar, , mataimakin shugaban APC na kasa reshen Kudu maso Kudu Ntufam Hillard Eta cewa yayi  jam’iyyar bata da wani zabi illay iyaka ta amince da hukuncin da kotun kolin ta zartar.

 Eta ya ce jam’iyyar mai mulki tana da darussa sosai da za ta koya daga abinda ya faru a Zamfara tun daga lokacin zabukan cikin gida

Jigon na jam’iyyar na APC ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a Abuja bayan taron kwamitin gudanarwa na jam’iyyar  inda ya kara da cewa jam’iyyar mai mulki ba ta da wani zabi sai dai ta amince da hukuncin da kotun koli da zartar na soke nasarar da tayi a zaben gwamna da ‘yan majalisun jihar da tarayya a jihar Zamfara.  

 A waje daya kuma ‘yan jam’iyyar adawa ta PDP suna can suna ta murna kan wannan hukunci na Kotun kolin, shi kuma tsohon dantakarar shugaban a karkashin inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar cewa yayi gaskiya c eta fara nuna halinta.  

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0