Ana Shirya Zanga Zanga Domin Ganin an Kori Manyan Hafsoshin Soja- Inji Fadar Shugaban Kasa.

Ana Shirya Zanga Zanga Domin Ganin an Kori Manyan Hafsoshin Soja- Inji Fadar Shugaban Kasa.

Daga Mohammed Lawal :

Jiya Asabar ne fadar shugaban kasa ta furta cewa ‘yan siyasa sa masu amfana daga kungiyar Boko suna nan suna kokarin shawo kan jama’a maza da mata kimanin dubu biyu domin su fito su gudanar da zanga zanga ranar litinin da nufin ganin an sauya manyan hafsoshin sojan Nijeriya.

Babban mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin jarida, Garba Shehu ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta samu rahotanni kan wannan aniya, inda ya kara da cewa irin wadannan mutane sune suka tara wasu tsirarun jama’a suka yiwa shugaban kasa ihu a lokacin da ya kai ziyara a Maiduguri, fadar gwamnatin Borno.

Garba Shehu yace yanzu haka wadannan gungun ‘yan siya da masu amfana daga kungiyar Boko Haram suna nan su rarraba kudi ga jama’a domin shawo kansu da su fito domin gudanar da zanga zangar. Kimanin mutane maza da mata dubu biyu aka dauki hayarsu domin gudanar da wannan zanga zanga ranar litinin da nufin ganin an sauya wadannan hafsoshin sojan Nijeriya.

 Yace yanzu haka jam’iyyar PDP tana can ta kai komo a ofisoshin jekadun kasashen waje tana batanci ga gwamnatin Muhammadu Buhari. Suna duk abinda suke iyawa wajen nuna cewa ‘yan Nijeriya na goyon bayansu.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0