Ana Kyamar Sinawa  a Kasashen Duniya Saboda Coronavirus

Ana Kyamar Sinawa a Kasashen Duniya Saboda Coronavirus

Daga Mohammed Lawal :

Al’ummar kasar China sun shiga wani hali na kyama daga al’umomin kasashe daban daban na duniya sakamakon annobar nan ta cutar mashako, wadda aka yiwa lakabi da Corona da ta samo asali daga garin Wuhan na kasar China, kuma take ta yaduwa kamar wutar daji.

Wanna kyama kokuma kauracewa yin ma’amala da ‘yan kasar ta China a kasashen duniya sun hada da hanasu shiga shagon sayayya, kin zama kusa da su a cikin motar bas ko jirgin sama ko na kasa, hana yara ‘yam makaranta cudanya da ‘ya’yan Chinese da makamantan hakan.

A karshen watan Janairun da ya gabata ne wasu jaridu suka buga labarun kin jinin Sinawa mazauna kasar Australia. Daga ciki akwai jaridar Daily Telegraph da ake bugawa birnin Sydney, inda a shafinta na farko ta yi kira ga Sinawa mazauna birnin na Sydney da su janye ‘ya’yansu daga makarantu, domin kada su yada cutar ga sauran dalibai.

Hakanan ita ma wata mata ‘yar shekaru 22 wadda tana da ruwan China, ta koka bisa ga yadda ake ta rubuto mata sakonnin batanci tun bayan da cutar ta corona ta barke,

A kasar Ingila ma Sinawan suna fuskantar tozartawa, domin kuwa a cikin jirgin kasa a birnin London, wani dalibi na jami’ar Royal Halloway ya sha zagi ta uwa ta uba daga fasinjoji, an kuma samu rahoton irin wannan ta faru a cikin jirgin karkashin kasa a kan wasu sinawan. Baya ga wannan harkokin kasuwanci a unguwar nan da ake kira China Town a Landan sun tsaya cik sakamakon kauracewa unguwar da jama’a sukayi.

A kasar Canada, labarin duk daya ne game da kyamar Sinawan, inda a kafar sada zumunta ta Instagram ake ta yada sakonni na kiran jama’a da su kauracewa gidajen sayar da abinci na Sinawa, wasu ma har suna shagube cewa mu bama cin jemage, jemage shine ya haifar da wannan cuta.

A Faranasa sa Jamus kuwa ba Sinawa ne kadai ke fuskantar wannan kyama ba, duk wani dan yankin Asiya yana cikin halin kunci da takura, yayin da jama’a ke yawan zolayarsu da yada kalamai na batanci gare su.

A Hong Kong kuwa ana hana Sinawan shiga gidajen cin abinci bisa ga dalilin cewa basu so a korar masu hudda dasu, akan fadawa Sinawan cewa muna son rayukan mu, bamu shirya mutuwa ba.

Zanga zanga aka gudanar a a gaban wani Hotel a Bukittinggi, na kasar Indonesia, domin kin karbar baki masu yawon shakatawa da suka fito daga kudancin China, Hakanan kuma masu zangan zangar sunyi kira da a killace Sinawan a cikin hotel har zuwa safiya sannan a maidasu filin jirgi su koma kasarsu.

 Kafafen sada zumunta a Japan kuwa aika sakonni suke tayi na yin kashedi ga Sinawa da kada su zo Japan, yayi da a wani gidan cin abinci kuwa jama’a suka yi ta eho ga wata mata ‘yar China, ba arziki ta fice daga gidan.

A North Macedonia kuwa kuskure akayi, inda wasu gungun matasa sukayi ta yiwa wasu ‘yan kasar Korea ta kudu ihu, suna zaton Sinawa ne.

Sauran kasashe na nahiyar Asia  kamar su Philipines, Singapore, Korea ta kudu suma sun dukufa wajen nuna kyama ga Sinawan, inda suke kira ga gwamnatocinsu su hanawa Sinawa shiga kasashen nasu.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0