An Yi Hasashen Samun Ruwa Sama Mai Yawa Da Zai Haifar Da Ambaliya  A Daminar Bana

An Yi Hasashen Samun Ruwa Sama Mai Yawa Da Zai Haifar Da Ambaliya A Daminar Bana

Daga Kabiru Yusuf, Abuja

Hukumar kula da Yanayin ta Najeriya  (NiMet) ta yi hasashen samun ruwan sama mai yawa a bana, tare Jan hankalin masana yanayi da sauran Al’uma da su dauki matakin kare kai gani da kulawa.

Hukumar tace za’a fara ruwa a karshen watan Fabrairun nan wanda ake kira daminar karya don haka kada manoma su ce zasu yi shuka a wannan lokaci.

Tace za’a  kwashe kwanaki 110 zxuwa 160 ana arewa a yankin artewacin Najeriya, yayinda a kudanci kuma za’a dauki tsawon kwanaki  210 zuwa 280 ana tafka ruwa a daminar ta bana.

Hukumar ta bayyana hakan ne a takardar bayananta da ta bugawa kan yadda yanayin shekarat 2020 ta ce zai kasance.

“Akwai alamun da ke nuni da cewa, a bana za’a samu ruwan sama isasshe. Don hak yana da kyau masana yanayi da kuma aAluma su yi shiri ko da za a samu yawan ruwa da ka iya jawo ambaliya da sauran matsalolin da akan samu a yayin damina.

To sai dai hasashen ya nuna za’a samun dan karamin fari a tsakiyar daminar, lokacin da ruwa zai dauke na makwani, don haka sai manoma su rinka barin yar ciyawa ko a haki a gindin yabanya don kare bushewa.

” Irin wannan yanayi a wasu lokuta kan raba wasu mutane da mahallansu baya ga haifar da wasu chututtuka da ka ita samu sakamakon ambaliya da Isa mai karfi da ake samu a lokuta da dama, inda har a wasu lokuta da tashin ruyuka da dukiyoyi.” A cewar hukumar.

Hukamar data ce yanayin zai haifar da zafi tun daga watan Janware zuwa Afrilu ta kara da cewa za’a iya samun daukewar damina da wuri a wasu wararen, wanda hakan kan iya haifar da fari

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0