An Samu Mutuwa ta Farko Daga Cutar Coronavirus a Nijeriya.

An Samu Mutuwa ta Farko Daga Cutar Coronavirus a Nijeriya.

Daga Mohammed Lawal  :

Da sanyin safiyar yau Litinin ne cibiyar kula da dakile yaduwar cututtuka ta Nijeriya (NCDC) ta sanar da mutuwa karo na farko daga cutar Coronavirus a Nijeriya. 

Cibiyar ta NCDC tace mutuwar ta faru ne a kan wani mutun dan Nijeriya mai shekaru 67 wanda ya dawo gida Nijeriya bayan wani balaguro da yayi zuwa Turai domin jinya kan wasu cututtuka da yake fama dasu da suka hada da hawan jinni da ciwon suga.

Iyalan marigayin, mai suna Suleiman Achimugu, wanda tsohon daraktan gudanarwa ne nakamfanin tallata bututun man fetur na Nijeriya, sun ce ya rigamu gidan gaskiya ne da misalin karfe 2 na daren Lahadi, 22 ga wannan wata na Maris.

Mai magana da yawun iyalan maragayin,  Abubakar Achimugu, ya ce tun komowarsa gida Nijeriya ne daga Birtaniya, Suleiman ya killace kansa, sannan ya kira cibiyar NCDC ya shaida mata cewa yana jin alamun Covid19, inda kuma aka auna shi aka tabbatar da yana dauke da kwayoyin cutar ta Covid 19.

Da aka tabbatar  yana dauke da Coronavirus, cibiyar ta NCDC ta garzaya dashi zuwa asibitin kwararru dake Gwagwalada domin yi masa magani, inda daga bisani yace ga garinku.

Yanzu haka dai iyalan marigayin ana can an killacesu a gidansu, sannan kuma cibiyar ta NCDC ce zata dauki alhakin yiwa marigayin jana’iza.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0