An Samu Mutun na Farko da ake Zargi Dauke da Cutar Corona a Jihar Katsina

An Samu Mutun na Farko da ake Zargi Dauke da Cutar Corona a Jihar Katsina

Daga Mohammed Lawal :

A karo na farko, ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Katsina ta samu mutun da ake zargin yana dauke da cutar Corona a garin Dutsinma.

Da yake jawabi ga manema labaru da safiyar yau Laraba, babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Katsina, Dr. Kabir Mustapha yace mutumen da ake zargi dauke da wannan cuta ta Corona, wanda yanzu haka an killace shi, kwanan nan ne ya dawo daga kasar Malaysia, kuma ya fara nuna alamun kamuwa da cutar, amma ana gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tuni dai an dauki samfarin jininsa domin gudanar da gwaje gwajen da suka wajaba, kuma gobe ne ake sa ran samun sakamakon. Kuma da zaran an tabbatar da yana dauke da wannan cuta za’a fara gudanar da neman mutanen da yayi ma’amala dasu.

 Ya kara da cewa ma’aikatar lafiya ta jihar Katisna tana nan tana aiki kafada da kafada da cibiyar binciken cututtuka ta kasa a kan wannan lamari.

Babban sakataren ya shawarci al’ummar garin Dutsinma da suyi taka tsan tsan wajen mu’amala da mutune, musamman a cikin taron jama’a.

Ya kuma ja hankulan jama’a fa su garzaya cibiyoyin kiwon lafiya domin neman taimako ko shawarwari dangane da matakan kare kai daga wannan cuta.

Yanzu haka dai a fadin Nijeriya akwai mutane ukku da aka tabbatar da sun kamu da wannan cuta ta Corona. Kuma yayin da aka tabbatar da wannan cuta kan wannan mutume na Dutsinma, zai kasance mutun na hudu Kenan.

Ministan Lafiya na Nigeria, Dr. Osagie Ehanire ya bayyana cewa mutum na ukku da aka samu dauke da wannan cuta wata matace ‘yar Nijeriya mai kimanin shekaru 30 da ta dawo daga Birtaniya ranar 13 ga wannan wata na Maris.Baya ga wani dan kasar Italiya da abokin aikinsa a wani kamfani dake jihar Ogun.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0