An Rufe Wani Shagon ‘Yan China a Abuja  Don Kaucewa Cutar Corona.

An Rufe Wani Shagon ‘Yan China a Abuja Don Kaucewa Cutar Corona.

Mahmood Sadeeq

Hukumar a Abuja sun rufe wani shago mallakar ‘yan kasar Sin watau China, inda aka gano sun shigo da kayayyakin abinci dangin kifi ta haramtacciyar hanya.

Ma’aikatar hukumar kula da kare ‘yancin masu sayen kayayyaki ta Najeriya ce ta dauki matakin a Larabar nan, domin kare shigo da cutar Corona kasar.

Ana can dai ana gudanar da bincike a kan wannan lamari, inda jami’an hukumar ke duba kayayyakin domin tabbatar da ingancinsu.

Kara Daukar Matakai na Kare Shigowar Corona

Dama dai gwamnatin Najeriya ta bayyana daukar karin matakai a kan cutar ta Corona, inda ta nada wani kwamiti mai karfi.

Ministan kula da lafiya na Najeriyar Osagie Ehinare ne ya bayyana hakan a Abuja. Yace kwamitin ya hada da jami’an kula da lafiya da na tsaro da kuma na ma’aiatar kula da harkokin sufurin jiragen sama.

Kwantar Da Hankali

Najeriya dai na kwantar da hankalin al’umma a kan cutar ta Corona, bisa cewa ba abin tada hankali bane, domin an dauki matakan da suka dace a kan wannan matsala.

Cutar ta Corona da ta samo asali daga kasar China ta sanya kasashe  da dama daukar matakai na kariya.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0