AN DASA GYAURON ‘YAN PDP NA AIKIN LEKEN ASIRI A CIKIN GWAMNATIN APC

AN DASA GYAURON ‘YAN PDP NA AIKIN LEKEN ASIRI A CIKIN GWAMNATIN APC

Wani bincike ya bankado yadda aka dasa wasu ‘yayan jamiyyar PDP a cikin gwamnatin APC ta Najeriya suna yiwa jamiyyarsu liken asiri.

Wasu ‘yayan jam’iyar APC sun kai ga fasa kwai mai doyin gaske a kan abinda suka kira  taimakawar da wani na hannun daman minista na musamman yake yiwa jam’iyar adawa  ta PDP ta hanyar yi mata leken asiri daga gwamnatin APC.

Mai taimakawa Ministan,  wanda malamin jami’a ne, yana daukan sirrin gwanatin tarayya wajen taimakawa jihar PDP a matsayin sa na dan kwamitin kwararru na jam’iyar PDP din.

A wani bangaren kuma Shi wannan mataimakin yayi amfani da sanaiyar da ya samu da kungiyoyin tallafawa ita wannan ma’aikatar, ya hada wadannan kungiyoyin da ‘yan kwamitin kwararru na PDP harma sun kai wadan nan kungiyoyin jihar Adamawa (daya daga cikin jihohin PDP) don tallafa mata da kudade.

Wata majiya ta ce jam’iyar PDP ta wakilta wannan mataimaki don wargaza shirin fara wani mahimmin tsarin tallafawa tattalin arzikin Nigeria.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0