Abba Kyari ya Rasu Bayan Fama da Cutar Corona

Abba Kyari ya Rasu Bayan Fama da Cutar Corona

Mahmood Sadeeq Abuja

Fadar shugaban Najeriya ra sanar da rasuwar shugabana ma’aikata na fadar gwamnati Mallam Abba Kyari sakamakon cutar Corona. A sanarawar da mai baiwa shugaban Najeriya shawara a fanin yada labaru Femi Adeshina ya sanar, yace marigayi Abba Kyari ya rasu ne a ranar Juma’ah a birnin Lagos inda yake jinya.
Abba Kyari ya kamu da cutar Corona ne sakamakon wata ziyarar aiki da ya kai kasar Jamus,  a ranar 20 ga watan Maris aka gano ya kamu da cutar bayan da aka gano ya kamu da cutar a lokacin da ya sanar da cewa ya koma Lagos domin ci gaba da kula da lafiyarsa bisa shawarar likitoci, kuma don kaucewa kara dora nauyi ga tsarin lafiyar Najeriya.
Shine mutum na farko mai rike da babban mukami a Najeriyar da wannan cuta ta Corona ta yi dalilin mutuwarsa. Sanarwa tace za’a sanar da janaizarsa nan gaba kadan.
An sanar da mutuwar Abba Kyari a dai dai lokacin da cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya ta sanar da samun karin mutanen da suka kamu da cutar da a yanzu suka kai 493, hukumar tace a ranar juma’a an samu karin mutane 51 da suka kamu da cutar. 

Wanene Marigayi Mallam Abba Kyari 

An dai haifi marigayi Abba Kyari ne a 1938, asalinsa dan kabilar Kanuri ne, babu cikakken bayani a kan rayuwarsa lokacin da yake yaro, amma dai an san a 1980 ne ya kamala digirinsa na farko a fanin nazarin hallayar bani adama a jami’ar Warwick da ke kasar Ingila, daga nan ya karanta aikin lauya a jami’ar Cambridge duka a Ingila.
Ya yi aiyyuka da dama da suka hada na lauya da aikin jarida da sashin kula da mulki da dai sauransu. A 2015 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa, mukamin da ya rike har zuwa rasuwarsa. Allah ya jikansa Ameen. 

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0