Mutanen Batsari sun kwashi gawarwaki 18 zuwa fadar Sarkin Katsina.

Mutanen Batsari sun kwashi gawarwaki 18 zuwa fadar Sarkin Katsina.

Mohammed Lawal

Daruruwan matasane daga karamar hukumar Batsari suka afka a gidan gwanatin jihar Katsina dauke da gawarwakin mutane goma sha takwas da ‘yan bindiga suka hallaka jiya talata  domin nuna takaicinsu bisa ga yadda sha’anin tsaro yayi matukar tabarbarewa a jihar Katsina.

Daga gidan gwamnatin kuma matasan suka nufi fadar Sarkin Katsina Dr. Abdul Muminu Kabir suna zanga zanga bisa ga yadda yanayinnarashin tsaro yake ci gaba da lalacewa a yankin nasu.

Matasan masu zanga zangar wadanda suka hawo babura da matoci biyar zuwa Katsina sun zargi jami’an tsaron da gazawa wajen samar da kariya ga al’ummomin yankin.

 A fadar sarkin Katsina ne dai aka gudanar da jana’izar mutanen su  18 da ‘yan bindigar suka hallaka a karamar hukumar Batsari a ranar larabar nan.

COMMENTS

WORDPRESS: 0
DISQUS: 0